ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Thursday, 12 April 2018

  Ayyukan Imam Ali (a.s) A Madina:

  Ayyukan Imam Ali (a.s) A Madina:

  Farkon abin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya fara aiwatarwa yayin da ya isa Madina shi ne gina Masallaci, don ya zama helkwatar Musulmi kuma cibiyar gwamnatin Musulunci. Sannan sai ya kulla 'yan'uwantaka tsakanin Muhajirai (da suka zo daga Makka) da Ansar (Mutanen Madina), don gina sabuwar al'umma a bisa asasin taimakekeniya, kauna da tausayin juna. Haka dai Manzo (s.a.w.a) ya 'yan'uwantar da kowane daya daga Muhajirai ga kowane daya daga Ansar, sai kuma ya kulla tashi 'yan'uwantakar da Ali Dan Abi Dalib (a.s).

  Idan muka bi diddigin wannan marhala ta wannan sako na karshe, za mu sami rawar da Ali (a.s) ya taka a cikin ta ba wanda ya taka irin ta ko kusa. Ya kasance a sahun gaba-gaba a dukkan yakokin Musulunci tare da makiyansa, ba wai wajen halarta ko yin yakin kawai ba, a'a da abin da ya gabatar na gwarzontaka da sadaukar da kai irin wadanda babu wanda ya gabace shi a cikin su.

  Hakika Imam Ali (a.s) ya halarci dukkan yakokin Manzon Allah (s.a.w.a) in ba yakin Tabuka ba, wannan kuwa bisa horon Annabi (s.a.w.a) ne, ya kasance ya taka muhimmiyar rawa a dukkansu, ban da ma wadanda shi ya jagorance su da kansa.

  Tarihi bai rubutawa Imam Ali (a.s) komai ba face sadaukar da kai da dagewa a duk matsayin da ya dauka, abin da ba shi ba wata fassara face abin da yake da shi na kasataccen yakini, zurfin taimako, dogara da Allah da bautarsa da kawar da kai daga wanninSa komai girmansa ko kankacinsa. Banda duk wancan, ga kuma baiwar da ya ke da ita ta daukakar himma, karfin kuduri da halin girma.

  Gudummawar da Ali (a.s) ya bayar wajen kare Manzon Allah (s) da kuma yaduwar Musulunci a garin Madina ba wai kawai ta tsaya ne ga batun yakukuwa ba, face dai akwai wasu batutuwan ma na daban da Ali (a.s) ya ba da tasa gudummawar sama da kowani sahabi daga sahabban Ma'aiki, Mai tsira da aminci.

  Mai son karin bayani yana iya komawa ga tarihin Manzon Allah (s) da muka tsara a wannan shafi, bangaren Abubuwan Da Suka Faru A Madina don karin bayani. Don kuwa shakka babu Ali (a.s) na da hannu cikin nasarar da aka samu.
  ____________
  (1)- Ibn Sa'ad ya ruwaito cikin Tabakat, juzu'i na 3, sashi na 1, shafi na 15, da isnadinsa daga Barra'u bin ?zib da Zaid bin Arkam, sun ce: "Lokacin yakin rundunar Usrah, ita ce Tabuka, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya cewa Ali dan Abi Dalib: Lallai ba makawa ko in tsaya ko kai ka tsaya. Sai ya halifantar da shi. Da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tafi yaki sai wasu mutane suka ce: Bai bar Ali ba sai don wani abu da ya kyamata daga gare shi. Sai labarin wannan ya je kunnen Ali (a.s.), sai ya bi Manzon Allah (s.a.w.a.) har sai da ya kai gare shi, sai ya ce masa: me ya zo da kai Ali? sai ya ce: ba komai Ya Manzon Allah, sai dai ni na ji wasu mutane na da'awar cewa wai ba ka khalifantar da ni ba sai don wani abu da ka kyamata daga gare ni.

  Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi dariya ya ce: Ya Ali, ashe ba ka yarda ka zama a wajena kamar Haruna a wajen Musa ba, ban da (kawai) cewa kai ba Annabi ba ne? sai ya ce na'am Ya Manzon Allah. Sai Manzon Allah ya ce: To hakika kuwa haka ne. Bukhari ya fitar da wannan hadisi a Sahih dinsa, da Muslim, Tirmizi, Ibn Majah, Hakim a cikin al-Mustadrik, Ahmad bin Hambali, a Musnad din shi, Nasa'i, cikin Khasa'is, Abu Na'im cikin Hilyatul-Awliya'i, Tabari, cikin tarihinsa, da Ibn Athir, cikin Usudul-Gabat, kamar yadda ya zo cikin Tarikh Baghdad da Kanzul-Ummal.

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#