ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Thursday, 12 April 2018

  BABBAR HIJIRA DAGA MAKKA ZUWA MADINA:

  BABBAR HIJIRA DAGA MAKKA ZUWA MADINA:

  Saboda ganin irin tasirin da Musulunci ke samu da kuma gazawarsu wajen dakushe haskensa, kafiran Makka sun shirya makirci na kokarin kashe Manzon ALlah (s).

  Bugu da kari kuma rasuwar Abu Talib, garkuwan nan na wannan jaririn addini, ya dauke wannan babban abin da ke kare su daga kashe Manzon (s). To sai dai kuma kafiran Makkan kulle-kullensu ba tare da la'akari da cewa Ubangiji Allah Yana sane da abin da suke kullawa ba.

  Don haka Allah Madaukakin Ya aiko da Mala'ika Jibrilu (a.s) da ya sanar da Annabin wannan mummunan kulli na kafiran, sannan kuma ya bukaci Manzon naSa da ya yi hijira ya bar Makkan zuwa Madina.

  Wannan umarni dai na Ubangiji ya biyo bayan taron da Kuraishawa suka yi a wajen taronsu na Darul-Nudwah , inda suka dace a kan kashe Annabi (s.a.w.a) ta hannun wasu gungu na 'yan iskan gari da ya kunshi mutum guda daga kowane babban gida daga gidajen Kuraishawa, don jinin shi ya tafi a banza; wato ya bace a tsakanin kabilu ta yadda babu wanda za a dorawa alhakin haka.

  Sai Kuraishawa suka yi kokarin gaggauta aiwatar da abin da suka dace a kai da daddare, sai dai Abu Lahab ya ba su shawarar aiwatar da wannan barna da sanyin safiya; don haka sai suka sa gidan Annabi karkashin matsanancin sa-ido don kar al'amari ya kufce daga hannunsu.

  Don haka da wannan dare ya yi sai wadannan 'yan iskan gari suka taru suka kewaye gidan Manzon Allah (s) da nufin aikata abin da suke son aikatawa da asuba. To a daidai wannan lokaci sai Allah Ya umarci Annabi (s) da ya fice daga gidan ya kama hanyar Madina, Ya kuma umarce shi da ya umarci Aliyu bn Abi Talib (a.s) da ya kwanta a kan gadonsa. Daga nan sai Manzon Allah Ya gaya wa Ali wannan umarni, sai Ali ya ce masa, shin za ka tsira idan na kwanta din, Manzo ya ce masa na'am, jin haka nan take sai ya kwanta a kan gadon ya rufu da mayafinsa, shi kuma Manzo ya ratsa tsakanin kafiran wadanda suke barci ya fita yana karanta fadar Allah:
  Muka kuma sanya wani shamaki a gabansu da wani shamaki a bayansu, sai muka lullubesu alhali ba sa gani . (Surar Yasin:9)

  Daga nan sai Manzon Allah (s) ya fita ya je ya samu daya daga cikin sahabbansa, wato tsohon abokinsa Abubakar bn Abi Kahafa, wanda saboda wasu dalilai ya ga bai dace ya bar shi a garin Makkan ba, don haka ya je ya same shi suka wuce, shi kuwa Imam Ali (a.s) ya ci gaba da kwanciyarsa cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tsoro ko fargaba. Su kuwa kafiran suka ci gaba da kewaye gidan a wasu lokuta suna lekowa cikin ganin Annabin don su ga ko yana nan, inda suka ganin Imam Ali a kwance amma suna zaton Manzon Allah ne.

  Daga karshe dai kafin wayewar gari wannan kungiya ta 'yan iska ta fada gidan Annabi (s) cike da amincewa da gudanar da wannan mummunan aiki. Amma duk da haka tsayuwa da suka yi cikin dare ya zama aikin banza, don kuwa wanda suke nema din ya riga da ya fita ya tafi, wanda suka gani ya fito daga cikin mayafi shi ne Zakin Allah Ali (a.s). Nan take cikin kunya da tsoro sai wadannan kafirai suka tambayi Imam Ali (a.s) ina Muhammadu ya ke, cikin kakkausar murya sai ya amsa musu da cewa: " Hala kun ba ni ajiyarsa ne? ". Ganin haka sai suka fita cikin kunya suka koma inda suka fito.

  Ta haka ne Allah Madaukakin Sarki ya kubutar da ManzonSa daga makircin mushirikai, kana kuma Ya fitar da shi cikin aminci daga cikin wadannan kafirai masu makauniya zuciya kuma ba tare da sun ganshi ba.

  Wannan lamari na kwanciyar Imam Ali (a.s) a kan gadon Manzo da kuma tsirar da Manzon ya yi a sanadiyyar haka dai yana da wani muhimmanci, domin ya bayyanar da irin matsayin Imam Alin da kuma irin tsananin sadaukarwarsa don kare tafarkin Musulunci da kuma rayuwar dan'uwansa Manzon Allah (s).

  Don kuwa Ali (a.s) ba tare da tsoro ba ya yarda ya kwanta a gadon Annabi, ya yarda ya sanya rayuwarsa cikin hatsari don Annabi ya tsira da ransa. Hakika idan har rayuwar Abu Talib (a.s) ta kasance garkuwa a kan kafiran Makka daga cutar da Annabi a wancan lokacin, to yanzu da ba ya nan ga jarumin dansa nan Ali ya cike wannan gurbi. A halin yanzu ga shi ya sadaukar da ransa don Annabi (s) ya rayu.
  Saboda irin wannan sadaukarwa da Imam Ali (a.s) ya yi ne ma Allah Ya saukar da aya, wadda take cewa:
  Kuma daga mutane akwai wadanda ke sayar da kansa don neman yardar Allah, Allah kuwa Mai tausayi ne ga bayi (Surar Bakara:20)
  Daga karshe dai Allah ya kawo karshen wannan makirci da kuma wadannan makirai, don kafin su ankara Annabi da abokin nasa sun fice daga Makka sun kama hanyar Madina. To amma don gudun kada kafiran su biyo su, sai suka buya a cikin wani kogo da ke kimanin mil uku daga kudancin garin Makka, wanda ake kira da kogon
  Thaur. Hakan kuwa aka yi don kuraishawa cikin gaggawa sun fito neman inda Annabin ya ke, inda suka iso har bakin wannan kogo, amma dai sai Allah Ya nufi wani gizo-gizo da ya yi saka a wajen, sannan ga wata tsuntsuwa kuma tana kwanci a bakin kogon ta yadda ba za a iya fahimtar akwai wani mutum a cikin kogon ba, don ba yadda za a yi mutum ya shiga cikin wannan kogo ba tare da kori wannan tsuntsuwa da kuma yaye wannan saka na gizo-gizo. To amma dai lokacin da suka iso wannan kogo dai, hankalin Abubakar ya tashi saboda tunanin abin da zai iya samunsu, har ma ya fara kuka, to amma sai Allah Ya saukar masa da nitsuwa a zuciyarsa don kada ya yi sanadiyyar kafiran su gano su, wanda hakan zai sa duk wannan kokari da aka yi a baya ya zamanto aikin baban giwa.
  Lokacin da kafiran suka sami tabbas din cewa babu kowa cikin wannan kogo, sai suka juya cikin yanke kaunar samun Manzon Allah (s). Ta haka ne Manzon Allah da abokin nasa suka fito suka kama hanyar Madina
  Bayan tafiya na 'yan kwanaki, Manzon Allah (s) ya isa wani waje dake wajen Madina da ake kira Kubah, inda ya ya da zango yana jiran isowar Ali bin Abi Dalib (a.s) da ayarin Fatimomin bani Hashim, wato Fatima mahaifiyarsa (Ali), Fatima 'yar Annabi, Fatima 'yar Zubairu bin Abdul-Mudallibi da Fatima 'yar Hamza. Lokacin da Ali (a.s) ya iso Kubah sai Manzo (s.a.w.a) ya tarbe shi, ya rungumi shi, har sai da hawaye suka zubo masa saboda tausayawa wahalhalun da ya sha akan hanya.
  Bayan isowar Imam Ali (a.s) Manzo ya saura a Kubah har na tsawon kwanaki biyu, a lokacin ne ma ya gina Masallacin Kubah bisa shawarar Ammar bin Yasir. Wannan ne masallacin farko a Musulunci. Daga nan sai Manzo ya hau abin hawan shi ya nufi Madina.
  Tarbar da aka yiwa Annabi dai lokacin da ya isa Madina ta kasance ta gama-gari ce. Dama mutane na jiran isowarsa. Lokacin da ya shiga garin sai mutane suka yi masa dandazo da ba a taba ganin irinsa ba. Mutane na rige-rigen haduwa da shi. Ya kasance ba ya wuce wani gida har sai mutanen gidan sun gayyace shi da ya shigo, sai dai shi ya kasance yana ce musu: " Ku ba taguwar hanya, domin hakika ita wadda aka yi wa horo ce ".

  Daga wannan hijira zuwa Madina ne aka fara kidayar kalandar Musulunci, wadda kuma malamai suka ce an yi ne ranar daya ga watan Rabi'ul Awwal. Amma abin mamaki yanzu makiya musulunci, sun mai da kidayar kalandar Musulunci watan safar.

  Yaye wasu shubuwohin sai in Ka'im (AF) ya bayyana Insha Allah.

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#