ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Thursday, 12 April 2018

  Irin tarbiyya da Imam Ali (a.s.) ya samu a gidan Ma'aiki (s.a.w.a)

  Irin tarbiyya da Imam Ali (a.s.) ya samu a gidan Ma'aiki (s.a.w.a)

  Irin tarbiyya da Imam Ali (a.s.) ya samu a gidan Ma'aiki (s.a.w.a) da kuma kusantarsa tun yana karami ya ba shi daman fahimtar al'amuran da manyan mutane suka gagara fahimta duk kuwa da cewa shekarunsa ba su taka kara sun karya ba.

  Kana kuma hakan ya ba shi daman samun tsarkakar zuciya, al'amarin da ya ba shi daman fahimtar gaskiya da kuma riko da ita, alhali kuwa sauran manyan mutane sun gagara fahimtar hakan, inda suka ci gaba da zama 'yan amshin shatan iyaye da kakanni, ...lalle mu mun sami ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mu, a kan gurabansu muke masu neman shiryuwa"

  A dai-dai wannan lokaci da Imam Ali (a.s.) ya komo gidan Manzon Allah (s.a.w.a.), kana kuma kulawarsa ta gaba daya ta koma hannunsa (s.a.w.a), Ma'aiki (s.a.w.a) ya kasance ya kan je bayan gari cikin wani kogo da ake ce ma "Kogon Hira" don tunani da kuma bautan Ubangiji.

  To a wannan lokaci kuwa babu wani mutum da yake zuwa wajensa in ban da wannan madaukakin saurayi, wato Imam Ali (a.s.) don kai masa abubuwan da yake bukata da kuma kasancewa tare da shi cikin wannan bauta na Ubangiji.

  To a cikin irin wadannan lokuta ne wani babban lamari ya faru ga rayuwa Ma'aiki (s.a.w.a), Imam Ali (a.s.) da kuma dukkan duniya baki daya.

  A dai-dai wannan lokaci da wannan babban lamari ya faru kuwa Manzon Allah (s.a.w.a.) yana da shekaru 40 ne a duniya, shi kuwa Imam Ali (a.s.) yana da shekaru 10 a duniya.

  Wannan lamari kuwa shi ne aiko Ma'aiki (s.a.w.a) a matsayin Annabi kana kuma Manzon Ubangiji ga dukkan duniya. Hakan kuwa ya biyo bayan zuwan Mala'ika Jibril (a.s.) ne da sakon Ubangiji, lokacin da yazo da aya ta farko ta Alkur'ani mai girma, wato:

  ﺇِﻗْﺮَﺃْ ﺑِﺂﺳْﻢِ ﺭﺑِّﻚَ ﺍﻟَّﺬِﻯ ﺧَﻠَﻖ + ﺧَﻠَﻖَ ﺍﻹِﻧْﺴﺎﻥَ ﻣِﻦْ ﻋَﻠَﻖٍ + ﺇِﻗْﺮَﺃْ ﻭَﺭَﺑُّﻚَ ﺍﻷَﻛْﺮَﻡُ + ﺁﻟَّﺬِﻯ ﻋَﻠَّﻢَ ﺑِﺂﻟْﻘَﻠَﻢْ + ﻋَﻠَّﻢَ ﺁﻹِﻧْﺴﺎﻥَ ﻣﺎ ﻟَﻢْ ﻳَﻌْﻠَﻢْ +

  Bayan faruwar wannan lamari, sai Ma'aiki (s.a.w.a) ya komo gida inda ya kira matarsa Nana Khadija (a.s.) da wannan dan'uwa nasa kana kuma abin kaunarsa, Imam Ali (a.s.) ya shaida musu abin da ya faru, wato aiko shi da wannan sabon addini na Musulunci.

  Nan take ba su yi wata-wata ba suka yi imani da shi kuma suka rungumi wannan addini da hannu bibbiyu.

  Ta haka ne Imam Ali (a.s.) ya zamanto musulmin farko kana ita kuma Nana Khadija (a.s.) ta kasance mace ta farko. Lalle ko ba a fadi ba wannan babbar falala ce da Imam Ali (a.s.) ya samu wanda babu wani sahabi da ya same ta.

  An ruwaito Salman Farisi (r.a) yana cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) yace: " Mutumin farko da zai sha daga tafkin alkausara a ranar lahira, shi ne wanda ya riga ku imani, (shi ne kuwa) Aliyu bn Abu Talib " .

  Imam Ahmad bn Hambal ya ruwaito cewa Ma'kal bn Yassar yace, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya gaya wa 'yarsa Fatima al-Zahra cewa: " Ya ishe ki abin farin ciki da alfahari cewa, na aurar da ke ga musulmin farko cikin al'ummata, sannan kuma wanda yafi hikima " ." .

  San kuma an ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa mutane uku, wato: Ezekiel, Habib Najjar da kuma Aliyu bn Abu Talib sun kasance mutanen farko da suka karbi kiran Annabawansu, (Annabi) Musa, Isa da kuma shi kansa, don haka ake kiransu da Siddikai .

  Sannan kuma Imam Ali (a.s.) yana cewa: " Ni na kasance bawan Allah kana kuma dan'uwan ManzonSa, sannan kuma wanda ya fi kowa imani da AnnabinSa. Babu wani wanda zai fadi haka, face makaryaci. Na yi salla a bayansa har na tsawon shekaru bakwai kafin wani yayi " .

  Wannan batu na kasantuwan Aliyu (a.s.) musulmin farko cikin al'umma Ma'aikin Allah (s.a.w.a.), al'amari ne da kusan dukkan malumman tarihi sun ruwaito shi kuma sun yarda da shi in ban da wasu ma'abuta son zuciya, wadanda suka bari son zuciya da kiyayya ga Ahlulbaitin Annabi (s.a.w.a.) suka yi musu katutu a zukatansu ta yadda suke karyata duk wata falala ta mutanen gidan Ma'aiki (s.a.w.a).

  Su wadannan mutane suna bayyana cewa kasantuwan Aliyu (a.s.) yaro ne dan shekara goma, a yayin wannan lamari, da wuya a ce ya mallaki hankalinsa ta yadda har zai iya bambance tsakanin karya da gaskiya, sabanin manyan mutane daga cikin sahabbai wadanda suka karbi Musulunci da girmansu. Su na ganin cewa ya karbi Musulunci ne kawai ba wai don zai iya fahimtar gaskiyar musuluncin ba, sai dai kawai don kusancinsa da Manzon Allah (s.a.w.a.), kasantuwan ya tashi ne a gidansa, don haka ya karbi Musuluncin.

  To amma abin da wadannan mutane suka gagara fahimta, ko kuma suka ki fahimta da gangan saboda abin da ke cikin zuciyarsu na hassada da kiyayya ga Mutumin da Manzon Allah (s.a.w.a.) yace babu mai sonsa sai mumini, kuma babu mai kinsa sai munafuki, shi ne cewa:

  1.
  Lalle kan Aliyu (a.s.) yaro ne a wancan lokacin, to amma yaro ne da ya kere yara irinsa (kai har ma da manya) kamar yadda ya kere manyan mutane a lokacin da ya girma. Don kuwa shi yaro ne da ya taso a hannun Annabin Rahama (s.a.w.a), wanda ya kere kowa wajen hikima da hangen nesa da kuma sanin ya kamata.

  Don haka da wuya, ko kuma a ce abu ne da ba zai yiyu ba, a ce wanda ya girma a hannunsa kuma ya sha daga tafkin ilimi da hikimarsa, zai zamanto kamar yadda su wadannan mutane suka bayyana.
  2.
  Kira zuwa ga imanin da Ma'aiki (s.a.w.a) yayi masa (a.s.) bayan dawowarsa daga kogon hira yana nuna mana cewa shi kansa Ma'aiki (s.a.w.a) bai yadda da cewa Aliyu (a.s.) yaro ne kamar sauran yara ba. Don kuwa ba mu gan shi (s.a.w.a) ya kirayi wani yaro zuwa ga Musulunci ba in ban da Aliyu (a.s.), abin da kawai muka gani yayi shi ne cewa yana gayyatar manyan mutane ne zuwa ga Musulunci, don sanin cewa 'ya'yayensu za su bi. To amma da ya zo kan Aliyu sai ya kira shi da kansa, don sanin cewa shi ba kamar sauran yara yake ba.
  3.
  Hakika da ace al'amarin haka yake, kamar yadda wadannan mutane suke gani, ai da Manzon Allah (s.a.w.a.) bai zabe shi a matsayin mataimakinsa kana kuma wazirinsa a lokacin yana shekara sha uku (13) a duniya ba, lokacin da aka umurce shi (s.a.w.a) da ya kira makusantansa zuwa ga Musulunci. (Za mu ga cikakken bayani kan wannan lamari a nan gaba).

  Don haka, bisa la'akari da wadannan abubuwa da muka kawo da ma wasunsu, za mu fahimci rashin ingancin da'awar wadannan mutane dangane da wannan lamari.

  Bayan wannan aike na annabci, Annabi (s.a.w.a.) bai kira kowa zuwa ga Musulunci ba har tsawon shekaru uku in ban da wadannan mutane biyu da suke tare da shi, wato Imam Ali da kuma matarsa Nana Khadija (a.s.). A takaice dai Musulunci ya kasance ne a tsakanin wadannan mutane ba tare an bayyanar da shi ba.
  ____________
  (1)- Surar Zukhruf 43: 22.
  (2)- Mustadrak al-Hakim, juzu'i na 3 shafi na 112.
  (3)- Musnad Ahmad, juzu'i na 3, shafi na 136.
  (4)- Ahmad bn Hmabal cikin al-Munakib, Nisa'i cikin al-Khasa'is da kuma Hakim cikin al-Mustadrak.
  (5)- Sunan ibn Majah, juzu'i na 1 shafi na 44, hadisi na 120, Riyadhun Nadhrah, juzu'i na 2, shafi na 158.

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#