ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Sunday, 29 April 2018

  JARABAWA CE KOWANNEMU ANA NAN ANA JARABTA SHI

  JARABAWA CE KOWANNEMU ANA NAN ANA JARABTA SHI

  _________Sayyid Zakzaky

  Ka ga wadannan jarabawowin suna nan har yanzu Allah (T) yana jarraba mu da jarabawowi, ya ga cewa ko kai ahalin wannan ne? Dubi inda Allah (T) yake tarbiyyar Manzonsa a cikin Surar ya ayyuhal muzzamil. Yana cewa inna sa nulkee alaika kaulan sakeela. Bayan da ya ce masa ya tsaya da sallar dare. Kumillaila illa kalila nisfahu auwinkus minhu kalila auzid alaihi wa rattilil kur'ana tartila, inna sanulkee alaika kaulan sakeela. Za mu jefa maka zance mai nauyi. Masu fassara sun ce ma'anarsa shi ne aiki da abin da aka umurce ka, aka hana. Wato kai ne za ka zama kyakkyawan siffa na duk abin da aka ce a yi. Alhamdu lillahi kuma haka Manzon nan ya kasance. Duk abin da Alkur'ani ya ce a yi shi ne mafi kyawun misali na aikata wannan.

  Wato kenan jarrabawa ce wanda kuma kowannenmu ana nan ana jarabta shi. Za a jarabta ka da kayan kwadayi. Kun san jarabawa yadda ake yi? Da ana yin jarrabawa yadda yake ba za ka iya ci ba, to da bai zama jarrabawa ba. Da kuma za a yi jarabawar da kowa ma zai ci, ba wanda ba zai ci ba. Kamar a ce in kana jin yunwa ka ci abinci. Wanene ba zai ci wannan jarrabawar ba? Ai ba jarrabawa ba kenan ko? Jarrabawa ita ce, kana jin yunwa kada ka ci, to jarrabawa kenan. Ko kuma kana jin kishi kar ka sha ruwa. Kamar wadanda aka jarabta su din nan, jama'ar Dalut (AS), wanda kafin su je su kara da jama'ar Jalut, jabberi.

  Bayan sun shawo rana, sun yi tafiya sun shawo rana, sai aka ce ga su nan za su gangara gulbi akwai ruwa, amma kada a sha. In kuma an hayyake gulbin za a hadu da makiya za a fafata yaki. Amma in an gangara aka kalli ruwan, a kalla kawai a wuce. Amma in ka kasa daurewa, ka ga ba za ka iya ba, to ka kamfata sau daya, shi kenan ka wuce, kar ka yi kamfata biyu da hannuka. Sai wasu suka ce "a'a to in mun hayyake ba za mu yi karo da makiya bane?" A ka ce Eh. "To!" Ba in muka sha ruwa ba sai mu sami karfin yaki? Aka ce, to ai Allah ne ya ce kar sha ruwan.

  To ka ga Innallah mubtaleekum bi nahar faman shariba minhu fa laisa minnee wamanlam yad'amhu fa innahu minnee illa manigtarafa gurfatan bi yadih. Sai dai wanda ya yi kamfata daya rak, to shi yana tare da wannan Manzo. Ka ga wannan ba karamar jarabawa bace. Ka kwaso kishi, ka ga ruwa a ce kar ka sha. Amma ka ga wasu sun ci jarabawar.

  Kadan ne kuwa suka ci wannan jarabawar. Sai wasu suka wuce suka yi dauriya na sosai. Suka ce tunda yake dai an ce kar mu sha, ba za mu sha ba. Sai wasu suka ce ai an ce ka kamfata daya, suka dan kamfaci daya din suka wuce.

  Mafi yawa suka kwankwada. Da suka hayyake, sai wadanda suka kwakwadi ruwan nan suka hango Jaluta da jama'arsa suka ce, "a'a, a'a, la dakata lanal yauma bi Jaluta wa junudihi." Sai suka jiyo baya, suka ce wannan ai ba yaki bane, kashe mu kawai za su yi.

  Su kuwa wadannan wadanda ba su sha ruwan ba, da wadanda suka yi kamfata daya suka ce kam min fi'atin kalilatin galabat fi'atan kasiratan bi izinillah wallahu ma'assabireen. Sai suka yi nasara a kansu suka rinjaye su da izinin Allah. Ya zama yakin ma dai Allah ya yi masu.

  DOLE A JARABTA KA DA ABIN DA YAKE DA WAHALA

  To, kun ga in Allah (T) ya gwada ka, abin da yake so da kai ka ci jarabawa, in ka ci shi kenan an gama, sai lambar yabo.

  To, dole kuwa in za a jarabta ka dole kuwa a jarabtaka da abin da yake da wahala. Kun san ko jarabawar da ake yi a makarantu, ya jarabawa take? In aka rubuta jarabawa kowa ya ci dari bisa dari ya zama jarabawa? Lokacin ina makaranta a Kano, ni dai bai koyar da ni ba, amma mutumin yana da dan tabin hankali ana ce masa Abdulkadir, wani Bamisire. Wai shi jarabawarsa, imma mi'a bil mi'a wa imma sifir.

  Haka yake maki. In ya kyallara idonsa, da ma ba ya gani sosai, in ya ga rubutunka na da kyau sai ya ce mi'a faukal mi'a. Kuma ko ka amsa daidai in ya ga rubutun gaja-gaja sai ya ce sifir. Shi makinsa kenan, ko dai ka ci dari bisa dari ko ka ci sifili!

  Ni bai koyar da ajinmu ba, amma dai a shekarar da muke ya koyar da wasu, tunda muna da azuzuwa hudu na a shekara guda ABCD, to ya koyar da 'yan C da B suna ta kuka. Wani ya iya amma kuma dai ya yi rashin sa'a ran nan ziro ya samu.

  Wani kuma ya yi sa'a ya sami dari. Wani ma bai iya komai ba ya ce shi gaskiya bai gane Arabiyya din nan ba. Sai ya je ya sami wani littafi ya haddace wani shafi sai ya zo ya rubata shafin. Sai ya ce duk mi'a.

  To wannan ba jarabawa bace. Kyawun jarabawa (shi ne) ya zamana an tambaye ka wani abu ne wanda yake ko za ka iya ci ko za ka iya faduwa. In ya zama duk ci za ka yi, to ba jarabawa bace. In ya zama kuma duk faduwa za ka yi, shi ma ba jarabawa bace. La yu kallifullahu nafsan illa wus'aha. Saboda haka duk lokacin da aka sa jarabawa jarabawa da za ka iya ci. Kuma zai yiwu ma ka ci duk.

  To za a jarabtaka ne da abubuwa da daman gaske, wa la nabluwannakum bi shai'in minal khaufi wal ju'i wa naksin minal amwali wal amfusi wassamarat wa basshirissabreen. To ka ga jarabawowin kenan. Tsoro, za a jarabtaka da tsoro. Kun ga na farko akwai wadanda aka firgitar da su. Aka ce masu innannasa kad jama'u lakun fakhshauhum. Sai suka ji tsaro?

  Fa zadahum imanan wa kalu hasbunallahu wa ni imal wakeel. Su muminai ne aka zo ana ba su tsoro. Wani ya ce, "a'a kai! Za ku cimma runduna, ta shirya sosai, mayaka majiya karfi da muggan makamai."

  Wai yana so ya ba su tsoro. Kai yadda na gan ku nan za su yi loma daya da ku. Shi ya dauka muminai za su ji tsoro ne. Kawai sai ya ga ana ta fara'a. Ana Malam ya? Ashe yau kuma alhamdu lillahi za mu yi shahada, masha Allahu! Wannan shi ne abin da Allah da Manzo suka yi mana alkawari. Kuma Allah da Manzo sun yi gaskiya. Kodayake da Hausa ne.

  Ana cewa a cikin Alkur'ani ba a fadin haka nan. Idan ka ce Allah da Manzonsa sai ka ce ya yi gaskiya. Wallahu wa rasuluhu ahakku anyurduhu. Manzo ya ji wani ya ce Allah da Manzonsa, sai ya ce huma. Sai ya ce ka munana magana, ba a gwama Allah da kowa.

  Haza ma wa'adallahu warasuluhu wa sadakallahu warasuluhu. Ba a ce wasadaka ba. Wallahu wa Rasuluhu ahakku anyurduhu, ba yurduhuma ba. Wato in ka fadi Allah, ba ka gwama shi da kowa

  Mai Nakaltowa Isiya Sy

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#