ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Thursday, 12 April 2018

  Kula Irin Ta Annabci Ga Imam Ali (a.s) Har Tasowar Sa (As)

  Kula Irin Ta Annabci Ga Imam Ali (a.s) Har Tasowar Sa (As)

  Tun daga lokacin da wannan tawaga ta Fatima bint Asad, Abu Talib da Manzon Allah (S) suka dawo gida, Annabi (s.a.w.a.) ya kasance ba ya rabuwa da wannan jinjiri mai albarka (wato Imam Ali) saboda tsananin kaunarsa da yake yi da kuma irin matsayin da yake da shi a wajen Ubangiji da kuma irin yadda zai taimake shi a nan gaba wajen isar da sakon Ubangiji wanda za'a ba shi nan gaba, da kuma kare wannan sako na Musulunci kamar yadda aka saukar da shi bayan rasuwar Annabi (s.a.w.a.).

  Hakan kuwa ba don komai ba sai don Manzon Allah (s.a.w.a.) ya san babu wani mutum cikin al'ummarsa da zai iya yin hakan in ba shi ba.

  Don haka yake nuna masa kauna da soyayya da kuma kula da shi da kuma yi masa tarbiya, don saboda wannan babban aiki da zai fuskanta a nan gaba.

  An ruwaito cewa, don saboda cimma wannan buri na kula da Aliyu (a.s.) da kuma irin kaunar da yake nuna masa, ya bukaci Fatima bint Asad da ta dinga kwantar da Aliyu (a.s.) a kusa da inda yake kwanciya.

  Bayan haka kuma shi yake masa wanka, ya ba shi madara, sannan kuma in lokacin barcinsa yayi ya dinga jijjiga abin kwanciyarsa har sai yayi barci, kana kuma idan ya tashi ya dauke shi yana masa wasa da dai sauran nau'oi na nuna soyayya da kuma kula.

  A wasu lokutan ma idan ya dauke shi sai ya dinga cewa: " wannan shi ne dan'uwana kana kuma wasiyyina, mai kiyaye sirri na, mijin 'yar da na fi so kana kuma halifana a baya na ".

  To haka dai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ci gaba da rainon Imam Ali (a.s.) har zuwa girmansa. To amma da yake masu iya magana suna cewa, wai waka a bakin mai ita tafi dadi, bari mu ji yadda irin wannan kulawa ta Manzon Allah (s.a.w.a.) ta kansace ga Imam Ali (a.s.) daga bakin shi kansa Imam din.

  An ruwaito shi a cikin shahararriyar hudubar nan tasa da aka fi sani da " al-Kasi'ah " yana cewa: " Tun ina karami na kasance na kaskantar da sanannun larabawa kana kuma na ci nasara kan sarakunan kabilar Rabi'ah da Mudar. Hakika kun san irin matsayi da kuma kusancin da nake da shi da Manzon Allah (s.a.w.a.).

  Tun daga farkon rayuwa ta ya kasance yana so na ni kuma ina sonsa. Ya kasance ya kan dauke ni akan cinyarsa lokacin ina karami, don haka na kasance ko yaushe ina tare da shi, kuma ya kasance ya kan rungume ni a kirginsa.

  Ya kasance ya kan kwantar da ni kusa da shi a wajen kwanciyarsa, ina jin dumi da kuma kamshin jikinsa. Lokacin ina karami ya kan ciyar da ni abinci da hannunsa yana mai tattauna abincin ya sanya min a bakina. Bai taba samu na da karya cikin magana ko kuma kuskure wajen aiki ba.

  Tun lokacin kuruciyarsa, Allah Ya ayyana wani Mala'ika mai girma daga cikin Mala'ikunSa don kulawa da shi da shiryar da shi zuwa ga kyawawan dabi'u wanda ni kuma na kasance ina binsa sau da kafa kamar yadda dan rakumi yake bin mahaifiyarsa. Ya kasance ya kan koyar da ni wasu kyawawan dabi'u kuma ya umurce ni da in bi.

  Sannan Ya kasance ya kan tafi kogon Hira kowace shekara, kuma a daidai lokacin babu wanda yake ganinsa in ban da ni. Kuma babu wani musulmi a wancan lokacin in ban da Manzon Allah (s.a.w.a.) da Khadija, sai kuma ni na ukunsu.

  Na kasance ina ganin hasken wahayi da kuma Musulunci, kana kuma ina jin kamshin annabci. Na ji gunjin Shaidan lokacin da aka saukar (wa Manzon Allah (s.a.w.a.) wahayi).

  Sai nace Ya Manzon Allah, wani irin kara ce haka? Sai yace min: Ai wannan gunjin Shaidan ne lokacin da ya yanke kaunar za'a bauta masa. Hakika kana jin abin da nake ji, sannan kuma kana ganin abin da nake gani, sai dai kawai kai ba Annabi ba ne, to amma kai waziri ne kana kuma kana kan hanya ta alheri.... ".

  Wannan kalami na Amirul Muminin (a.s.) yana tabbatar mana da irin matsayin da yake da shi da kuma kulawar da ya samu a wajen Manzon Allah (s.a.w.a.) tun ranar da aka haife shi har lokacin da aka aiko shi (s.a.w.a) a matsayin Annabi. Hakan kuwa duk dai da nufin ya gina shi da kuma tabbatar da shi saboda irin babban aikin da zai fuskanta nan gaba. Don haka ne ya zamanto tilo cikin dukkan sahabban Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da kuma sauran mutane gaba daya.

  Malaman tarbiyya da sanin dan'Adam sun tabbatar da cewa, dukkan irin halayen da mutum ya sami kansa a cikin na daga kyawawan dabi'u ne ko kuma akasin hakan, suna samo asali ne daga irin tarbiyya da kuma kulawan da mutum ya samu tun yana karami.

  Ta yadda ana iya gane tafarkin da yaro zai bi da kuma yadda zai gudanar da rayuwarsa, idan aka yi la'akari da irin tarbiyyar da yake samu daga iyayensa ko kuma masu yi masa tarbiyya.

  Don haka, ba ma bukatan wani karin bayani dangane yadda halaye da kuma dabi'un Imam Ali (a.s.) za su kasance ko kuma suke, matukar dai muka yi dubi da irin halayen wanda yayi masa tarbiyya wato Manzon Allah (s.a.w.a.), wanda Allah da Kansa Ya shaidai shi da kyawawan dabi'u a cikin Alkur'ani mai girma: "Kuma lallai, hakika kana a kan halaye na kwarai" ".

  To saboda haka ne Imam Ali (a.s.) ya gaji dukkan wata dabi'a ta kwarai wanda Manzon Allah (s.a.w.a.) yake da ita, da suka hada da gaskiya, rikon amana, karimci, jarunta, sanin ya kamata, hakuri, sadaukarwa, tsantsaini, gudun duniya, girmama na gaba, girmama mata da yara, tausayawa 'yan'Adam, kula da hakkin mutane da dai sauran duk wasu nau'o'i na kyawawan halaye.

  ____________
  (1)- Nahjul Balagah, huduba ta 192. Sannan kuma Allamah Hilli ma ya ruwaito ta cikin Kashful Yakin, da dai sauransu.
  (2)- Surar Kalam 68: 4.

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#