ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Sunday, 29 April 2018

  Ranar da aka aiko annabi Muhammadu a matsayin Annabi

  Yau 27 ga watan Rajab da ya yi daidai da shekarar miladiyya ta 610 aka aiko Annabi (S) matsayin dan sako na karshe daga ubangiji.

  Isiya-Sy

  ranar da Allah madaukakin Sarki cikin rahamarsa ya aiko annabi Muhammad mai tsira da aminci da iyalansa zuwa ga jinin da yan-adam da sako.

  Rana ce da ta kawo karshen zamanin duhun jahiliyya da bata wanda mutane su ka yi shekaru masu tsawon gaske suna rayuwa a ciki.

  Hakika Allah ya yi baiwa ga muminai da ya aiko manzo a cikinsu daga kawunansu. Yana karanta ayoyinsa a gare su, yana tsarkake su,, yana sanar da su littafinsa da hikima, gaban aiko da shi sun kasance a cikin bata mabayyani.

  Rana ce wacce a cikinta ne wani daga cikin zuriyar annabi Ibrahim mai karya gumaka, ya bayyana domin ya tseratar da jinsin da yan adam.

  Amintacce ne kuma tsarkakke, wanda ya ke dauke da saqo mai haske yake kuma bada taken tauhidi, a ranar 27 ga watan Rajab da ya yi daidai da shekarar miladiyya ta 610 aka aiko shi a matsayin dan sako na karshe daga ubangiji. Sunansa mai albaka muhammadu tsira da aminci a gare shi da iyalansa. Yana dauke da gatari da annabi Ibrahim ya rusa gumaka a hannunsa, sannan kuma yana rike da sandar musa da kuma zuciya ta almasihu.

  Tamkar annabi Nuhu yana da azama wacce ta fi karfe karfi, da hakuri irin na Ayuba, da kuma kyawun halitta irin na annabi Yusuf.A kowane lokaci da ranar aiko ma'aiki ta ke zagayowa tamkar annabi muhammadu ne ya ke sake fitowa daga cikin kogon Hira dauke da sakon da aka saukar masa da littafin shiriya domin ya shimfida adalci a doron kasa bakidaya.

  Ya kuma kusantar da zukatan mutane su zama yanuwa, ya samar da hadin kai a tsakanin mutanen da su ke a tarwatse.

  Yana fitowa daga cikin kogon Hira saboda ya kawar da duhun sabuwar jahiliyyar da ta mamaye kowace kusurwa ta wannan duniya.

  Kai kace yana kallon wannan duniyar tamu da ta ke takama da ci gaban ilimi da kere-kere yana tambayar cewa: Bisa wane dalili ne ake kashe kananan yara da mata da ba su ji ba su gani ba a bangarori daban-daban na duniya, da suka hada Afirka da Palasdinu da Iraki?

  Annabi Muhammad ma'aiki ne daga ubangiji kuma mai ceton mutane. Shi ne babban malami ta fuskar kyawawan halaye da dukkan wani abu mai kyau.

  An aiko shi ne a cikin wata al'umma wacce ta wofinta daga duk wani ilimi. Wadanda su ka iya karatu da rubutu a cikinta basu wuce a kirga su da yan yatsun hannu ba. Bugu da kari al'umma ce wacce ta ke cike da zalunci ta yadda ma'abocin karfi ne ya ke iko.

  Annabi Muhammadu ya bude sabon shafin rayuwa a cikin wannan al'umma da ma jinsin dan-adam bakidaya.

  Sakon da ya zo da shi wanda kuma ya fara a cikin wannan al'umma ta larabawa mai amfani ne da kuma muhimmanci ga dukkan jinsin yan-adam baki daya. Ana da bukatarsa a cikin kowane lokaci da kuma kowane bagire.

  Ranar aiko ma'aiki mai tsira da aminci rana ne ta farkawa da kuma wayewa. Rana ce ta rayar da al'umma da bunkasar kyawawan halaye da dukkan wasu abubuwa masu kyau.

  Kogon hira wuri ne da annabi muhammadu ya ke yin halwa a cikinta a lokaci mai tsawo.

  A kowace shekara yana zama a cikin wannan kogon na tsawon wata guda domin yin tunani da samun nutsuwa da kadaici da mahalicci, sannan ya fito ya sake ci gaba da rayuwarsa a cikin al'umma.

  A lokacin da dare ya ke shigowa taurari su ke haske samaniya annabi muhammadu yana zama a cikin wannan wuri mai kadaici da kawaici nesa da hayaniyar birnin makka, domin yin sujjada ga mahaliccinsa.

  A wani lokacin yana kallon birnin makka bakidayansa daga kan wanann dutsen mai tsawo a lokacin da mazaunansa su ke bacci da kuma tsayuwar kai da komowa.

  Annabi Muhammadu ya bambanta da sauran mutanen makka ta fuskar halaye tun daga lokacin kuruciyarsa har girmansa. Bai dulmiya a cikin halaye na jahiliyya ba ko kadan. Rikon amanarsa ne ya sa mutanen makka su ka masa sunan Al-amin.

  Shekaru arbain na rayuwar annabi Muhammadu mai tsaira da aminci da iyalansa sun cika daidai. A cikin dare a lokacin da ya ke ci gaba da tunani mai zurfi, haske daga sama ya sauka acikin wata daga kusurwowin wannan kogo da kuma wata murya mai karsashi. Mala'ika jibra'ilu ne ya sauka da sako na musamman daga mahaliccin sammai da kassai zuwa gare shi. Ya fara magana da shi yana mai cewa: "Kai muhammadu annabin Allah ne, kuma ni ne Jibra'ilu.

  "A lokacin da annabi Muhammadu ya ke kallonsa cikin mamaki, mala'ika Jibra'ilu ya ci gaba da yi masa magana yana cewa:" Ka yi karatu."Annabi Muhammad ya amsa da cewa: "Ni ba mai karatu ba ne"Jibra'ilu ya ci gaba da yin kira ga annabi muhammadu da ya yi karatu,sannan ya ci gaba da cewa:" Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda ya yi halitta. Wanda ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu, ubangijinka ne mafi daukaka. Wanda ya sanar da rubutu da alkalami. Ya sanar da mutum abinda bai sani ba."Tare da cewa annabi muhammadu bai iya rubutu da karatu ba amma sakon farko da ya sauka a gare shi shine na ya yayi karatu.

  Da haka ne annabi muhammadu ya zama wanda Allah zaba domin ya dauki sakonsa na karashi zuwa mutane. Wannan lokacin kuma ya zama mabudin tauhidi da kuma samar da sauyi a cikin rayuwar mutane a doron kasa. Annabi muhammadu ya fara da kiran mutane zuwa ga tauhidi da wasti da bautar duk wanda ba Allah ba.

  Aiko da annabi Muhammadu wani sabon shafi ne a tarihin biladama a doron kasa. Sakon da ya ke dauke da shi ya shafi dukkanin jinsin danadam ne ba wata kabila guda ba. Dukkan wasu halaye da ya rika kiran mutane zuwa gare su sun riga sun zamar masa jiki tun kafin a aiko shi da sako. Gaskiya da rikon amana da sauran halayen yabo.

  Annabi Muhammadu ya zama mai nuna matuqar damuwarsa akan yadda mutanen makka suna dulmuye a cikin fasadi da barna. Su ke kuma dogaro da takobi a cikin komai domin warware sabanin da ke tsakaninsu maimakon magana da tattaunawa. Hakurin da Allah ya ba shi da kuma tsayin dakarsa sun zama abubuwan da su ka taimaka masa matuka wajen daurewa cutar da shi da mutanen makka su ka yi sabonda sakon da ya zo da shi.

  Domin kuwa sako ne da yake kira da rusa abubuwan da su ke baiwa tsarki kamar bautar gumaka da algusshu a cikin mu'amala da danne mai rauni.Da akwai manufofi da dama da su ke kunshe a cikin aiko annabawa.

  Sun hada da koyar da mutane kyawawan halaye da tsarkake zuciya da shimfida adalci da kawar da zalunci. Ya zo acikin kur'ani cewa:" Mun aiko da manzanninmu tare da hujjoji mun kuma saukar da littafi da mizani tare da su saboda su tsaida adalci a tsakanin mutane."Ajumlace aiko annabi yana da muhimman manufofi guda biyu: Na farko shi ne samar da sauyi a tare da mutum kuma daga cikin zuciyarsa. Annabi da ya ke dauke da tutar shiriya wacce ta ke bayyananniya tamkar rana yana nuna mutum hanyar da zai bi ya kai ga samun sauyi a cikin zuciyarsa da kuma rayuwarsa bakidya.

  Wata manufar kuwa ta aiko annabi shi ne kira zuwa ga tauhidi da kadaita Allah. An umarci annabi da ya shiryar da mutane su daina bautar gumakan da ne su ka kirkiresu su bautawa Allah makadaicin sarki wanda ya yi halitta.Abu ne da babu shakku a cikinsa cewa annabawa sune ja gaba wajen samar da sauyi a cikin jinsin biladama.

  Yin aiki da sakon da annabi muhammadu ya zo da shi kuwa shi ne mabudin ci gaba da shiriya a cikin rayuwar mutum.

  Annabawan Allah kama daga Isa da Musa da Muhammadu sune wadanda su ka aza tubalin ci gaba na kyawawan halaye da inganta ruhi wanda ci gaban danadam ke takama da su a wannan lokacin.

  Jinjina ga annabi Muhammadu wanda shine dan sakon karshe daga Allah.

  Daukaka ta tabbata a gare shi wanda shine mai tseratar da dukkan jinsin yanadam. Wanda kuma ya bude kofar samun sa'ada ga mutane.

  Daukaka da yabo su tabbata ga dukkan annabawan Allah masu shiryarwa,wadanda kuma su ke a matsayin abin koyi ga dukkan mutane.

  #ObeyCourtOder
  #🆓Zakzaky
  AllahProtecZakzak

  To find out detailed information on the event of Ahlul-Bayt (As), visit:

  🌐Webside
  Isiyasy.blogspot.com
  Isiyasy.WordPress.com

  💠 Telegram 
  http://t.me/F5StarMedia
  https://t.me/F5StarsMediaGroup

  https://mobile.twitter.com/Isiyasy
  http://mobile.fb.me/F5StarsMedia/ 

  https://mobile.facebook.com/F5StarsMedia/?

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#