ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Sunday, 29 April 2018

  tunawa da ranar da aka aiko annabi(s.a.w

  Ubangiji ya azurta kwanakinku cikin tunawa da ranar da aka aiko annabi(s.a.w

  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

  Wasu `ya tsirarun abubuwa da ka gutsiro daga littafin(sima`u rasulil a'azam fil kur'an)

  Tareda da alkalami sayyid adil alawi

  Manzon mafi girma cikin motsin al'umma:
  Idan manzon mafi karamci ya fuskanci wahalhalu daga jama’arsa sakamakon jahiltarsa da jahiltar matsayinsa madaukaki cikin dukanin marhaloli da daurori wadanda harkar muslunci ta gifta ta, babu banbanci ciin kasantuwarta gabanin aiko annabi ko bayan aiko shi ko kuma kafin hijra ko bayanta lokacin da yake araye ne ko bayan wafatinsa(s.a.w) lalle daga cikin abubuwan da suka biyo bayan wannan fakuwar saninsa ko ace gazawa ko kasawa wanda ya kai ga jahiltar girman matsayin annabin rahama da mtumtaka (s.a.w) da saninsa kamar yadda yake, musulmi sun koma baya sunci baya daga girmansu mai tushe da wayewarsu ta mutumtaka wadda ta game duniya baki daya da falaloli da karamci da ilimi da fannoni, sai gaba da kiyayya da rigimgimun mazhabobi da kabilanci wanda suke da tushe na jahiliyar farko suka maye gurbi, sai ya zamanto karfinsu ya kau sun gaza samu nasara sun fadi jarrabawa a fagagen cigaba da gabata har ta kai gab akin haure da karnukansu masu yi musu aiki daga sarakuna da shugabanni sun samu iko kan wuyayensu, sai su kasnce suna kwashe dukiyarsu
  suna shan jinanansu suna ci da guminsu su koma su raya kasashensu, su riketa matsayin taguwar da za ta kaisu ga manufofinsu da bukatunsu da maslahohinsu da shirye shiryensu na mallake raunana cikin duniya baki daya da kowanne irin yanayi ta kama.

  Babu wata al`umma da `daga ta kai ga gano martaba da matsayin manzo mafi girma a tsawon marhaloli da zamanunnuka da suka shude da gabata ballantana ace sun ka ga siffantuwa da dabi`unsa da sasanninsa da dabakokinsa, wajibi kan kowanne musulmi ya san yadda annabi(s.a.w) ya rayu da kuma tarihinsa mai cike da haske da ayoyin rahama da da tausayi da soyayya da `kauna lalle ya kamata ya san mu’ujizarsa dawwamammiya wato `kur’ani mai girma, kai ya kamata ace ay san sahabbansa wadanda sukai ma annabi(s.a.w) rakiya cikin halartuwarsa da tafiye-tafiyensa kai cikin dukkanin marhalolin rayuwarsa, sun kasance batattun da ya shiryar da su cikinsu akwai kunne da yake kiyayewa wanda shine sarkin muminai ali(as) lalle shi kamar yadda sukace shi aya ne daga ayoyin annabta Annabi (s.a.w) alle shi ya kasance mu`ujiza ta biyu bayan kur’ani mai girma wanda ke nuni zuwa ga gasgatar annabtarsa da girman sakonsa ta yadda kimomi suka taso daga tarbiyarsa kamar misalign sarkin muminai ali(as).

  Mai karatu cikin rayuwar manzon rahama da sannu zai ga akwai wasu manyan mutane da suke kusa da manzon rahama kamar misalin ali(as) abu zar gifari da ammar ibn yasir da mikdadu kai hatta hadisi ya zo daga manzon Allah(s.a.w) yana cewa salmanu daga cikinmu yake mu ahlul –baiti .

  haka manzon rahama yana cewa lalle Allah yana shaukinsu lalle aljanna ma tana shaukinsu, kadai dai sun samu wannan daukaka mai girma sabon sanin da sukaiwa manzon Allah(s.a.w) da sanin akamalrsa da kyawunsa basu taba yi masa jayayya ba kamar yadda wasu sukai cikin matsayarsa da hukuncinsa, su sun tsaya kyam tareda shi sakamkon karfafar imaninsu da shi dakuma kasantuwarsa wajen shi bai Magana da son zuciya face abinda akai masa wahayi.

  Dayansu bait aba fadi kamar yadda wancan mutumin ya fadi lokacin da annabi(s.a.w) zai yi wafati da yace akawo mas alkalami dan tawada da takarda domin ya rubuta musu wani abu da ba zasu bata a bayansa ba sai wannan mutum ya gane cewa annabi(s.a.w) yana ishara zuwa ga hadisin saklaini littafin Allah da tsatsonsa daga ahlul baiti wanda jagoransu ya kasnce sarki muminai ali(as) lalle manzon Allah(s.a.w) ya furta wannan hadisi a wurare da daman gaske

  ‏( ﺇﻧﻲ ﺗﺎﺭﮎ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﻟﺜﻘﻠﻴﻦ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻋﺘﺮﺗﻲ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ ﻣﺎ ﺍﻥ ﺗﻤﺴّﻜﺘﻢ ﺑﻬﻤﺎ ﻟﻦ ﺗﻀﻠّﻮﺍ ﺑﻌﺪﻱ ﺃﺑﺪﺍً ﻭﺍﻧﻬﻤﺎ ﻟﻦ ﻳﻔﺘﺮﻗﺎ ﺣﺘّﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲّ ﺍﻟﺤﻮﺽ

  Lalle ni mai barku muku nauyaya guda biyu ne littafin Allah tsatsona ahlul baiti matukar kunyi riko da su ba zaku taba bat aba bayana har abada lalle su biyun basu taba rabuwa da juna har sai sun gangaro wurina a tafki.

  Wannan ingantaccen hadisi ne mutawatiri daga dukkanin bangarori biyun shi’a da sunna. A wannan loakci sai wani mutum ya cewa manzon Allah(s.a.w) wai wannan mutumin ya zautu baya cikin hankalinsa wa’iyazubillahi daga wannan mumuna kalami nasa. Ina wannan mutumin za a hada shi da salmanu da misalsalinsa daga zababbun sahabban annabi(s.a.w) masu girman daraja yardadddun Allah.

  Babu shakka cikin kasntuwar nesantarwa da kusantarwa cikin matsayin manzon Allah(s.a.w) sun rukunantar da gurabe bayyanannu cikin mutanen da suka rayu da shi a kebance, haka da al`umma cikin gamewa duk wanda ya kasance mai adalci bai makantar da kansa cikin makauniyar biyayyar iyaye da sannan kuma zargin mai zargi bai da meshi ba lalle zai fuskanci wannan abubuwa da muka fadi zai dauketa a matsayin sako da nauyi dake rataye a wuyansa.

  Sai ta banbanta wurinsa da yanayin amsar da ya samu da sakamako bisa akidu da ka`idoji ingantattu da suka samu ingancins kan hsken kur’ani da ahlul baiti

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#