ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Thursday, 19 April 2018

  Zagayowar Ranar Haihuwar Imam Husaini {a.s} .

  Zagayowar Ranar Haihuwar Imam Husaini (As)

  Isiya-Sy

  Takaitaccen Tarihin Imam Husaini Dan Ali Dan Abi-Talib (As). Jagoran shiriya na uku daga cikin jerin jagororin shiriya goma sha biyu da Manzon tsira Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} ya yi bushara da samuwarsu a bayansa, kuma ya bayyana kasantuwarsu da daukakar addinin musulunci, sannan ya rubanya su da alkur'ani mai tsarki saboda tsarkakansu, kuma ya yi wasici wa al'umma da yin riko da su gaba daya, kuma ya siffantasu da jirgin tsira wanda ya hau ya kubuta wanda ya saba musu ya halaka, kofar tuba wanda ya shiga an gafarta masa, hujjojin Allah a bayan kasa, magada ilimin annabawa da manzonni, shi ne Imam Husaini dan Ali dan Abi-Talib {a.s}.

  An haifi Imam Husaini {a.s} ne a ranar uku ga watan Sha'aban shekara ta hudu bayan hijira a birnin Madinah, yayin da bushar haihuwarsa ta kai ga Manzon Allah {s.a.w} sai Manzon Allah ya hanzarta zuwa gidan 'yarsa Fatimatuz-Zahra {a.s} yake cewa Asma'u yar Umais da ta miko masa dansa, Manzon Allah {s.a.w} ya rungume shi cikin farin ciki da murna, sannan ya yi kiran salla a kunnensa na dama kuma ya yi ikama a kunnensa na hagun.

  Manzon Allah {s.a.w} ya tambayi Imam Ali dan Abi-Talib {a.s} sunan da ya sanya wa dansa, amma sai Imam Ali ya amsa da cewa; hakika ban kasance zan riga Manzon Allah sanya masa suna ba, don haka Manzon Allah {s.a.w} ya rada masa suna Husaini. Bayan cikan kwanaki bakwai da haihuwar Imam Husaini, Manzon Allah {s.a.w} ya tafi gidan Ali da Fatima ya yanka ragon suna ga dansa Husaini, sannan ya yi umurni da yi masa aski da yin sadaka da azurfa daidai da nauyin gashin da aka aske, kuma Manzon Allah ya bada umurni yi masa kaciya, kamar yadda aka gudanar ga dan uwansa Hasan {a.s}.

  Hakika Imam Husaini ya tashi ne tare da dan uwansa Imam Hasan a gida mai albarka kuma karkashin kyakkyawar kulawa na mahaifi da mahaifiya da kaka, domin Imam Husaini da ne ga shugaban muminai Imam Ali dan Abi-Talib {a.s} jagoran shiriya na farko bayan Manzon Allah {s.a.w} kuma mahaifiyarsa ita ce Fatimatuz-Zahra {a.s} yar Manzon Allah sannan kakansa shi ne Annabin rahama Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} da Allah ya aiko shi rahama ga talikai.

  Imam Husaini {a.s} ya rayu da kakansa Manzon Allah {s.a.w} na tsawon shekaru shida, don haka Manzon Allah ya dauki matakin tarbiyyantar da shi kyawawan dabi'unsa masu girma, inda Imam Husaini ya kasance ya kawatu da dabi'un Manzon Allah, saboda haka Imam Husaini ya kasance yana da babban matsayi a wajen Manzon Allah {s.a.w} don haka Annabin rahama ke bayyana shi da cewa: Husaini daga gare ni yake, ni ma daga gare shi na ke, Allah ya so wanda ya so Husaini.

  Bayan rasuwar Manzon Allah {s.a.w} Imam Husaini {a.s} ya rayu karkashin kulawar mahaifinsa shugaban muminai Imam Ali dan Abi-Talib {a.s} na tsawon shekaru talatin da uku, inda ya yi tarayya da shi a dukkanin gwagwarmayar da ya gudanar wajen shiryar da al'umma. Har ila yau a bayan shahadar Imam Ali dan Abi-Talib {a.s} Imam Husaini {a.s} ya kasance karkashin jagorancin dan uwansa Imam Hasan Al-Mujtaba {a.s} na tsawon shekaru goma, inda ya kasance tare da shi a fagen siyasa da zamantakewar jama'a.

  A bayan shahadar Imam Hasan Al-Mujtaba {a.s} ragamar jagorancin al'umma ta koma ga Imam Husaini {a.s}, inda ya gudanar da gwagwarmayarsa a fage da dama musamman fito na fito da gwamnatin zalunci, kokarin hada kan al'ummar musulmi, fayyace wa al'umma zaluncin masu mulki, kokarin dawo wa mutane da hakkokinsu, tunasar da al'umma hakkin da ya hau kansu da ilimantar da su hakikanin koyarwan addinin Musulunci da kakansa Manzon Allah {s.a.w} ya zo da shi domin 'yantar da mutane daga duhun kafirci da jahilci zuwa ga hasken shiriya.

  Matsayin Imam Husaini {a.s} Dangane Da Ibada. Hakika bautan Allah ita ce tushen rayuwa a wajen Imam Husaini {a.s} kuma zuciyarsa tafi ta'allaka da ita, Imam Husaini {a.s} ya rungumi bautan Allah tare da kaunarta a zuciyarsa, kuma ya kasance yana tarjamata a aikace da gabobinsa, kamar yadda ya kasance dukkanin rayuwarsa ibada ce.

  Tabbas Imam Husaini {a.s} ya kasance cikin bautan Allah dare da rana, a fili da boye, kuma ya kasance yana tsayuwa a gaban mahaliccinsa tsayiwar bawa da ya san kima da matsayin Ubangijinsa.

  Malaman tarihi sun ruwaito cewa:- Imam Husaini {a.s} ya kasance yana aikata duk wani abin da zai kusanta shi da Allah Madaukaki, domin ya kasance mai yawan salla, azumi, hajji, sadaka da sauran ayyukan alkhairi.

  Hakika Imam Husaini {a.s} ya kasance daga cikin jerin bayin Allah masu tsananin tsoronsa da kauracewa duk wani abin da ya kasance sabonsa, saboda tsananin tsaronsa ga Allah ake tambayarsa cewa: Wani irin tsananin tsoron Allah ka ke da shi ne? Sai Imam Husaini {a.s} ya amsa da cewa:- Hakika babu wanda zai samu aminci da tsira a ranar lahira sai wanda ya ji tsoron Allah a duniya.

  Imam Ali Zainul-Abidin {a.s} yana bayyana cewa: Mahaifinsa Imam Husaini {a.s} ya kasance a mafi yawan lokutansa a tsawon yini da dare yana tsayar da salla da gudanar da azumi, a cikin dare yana salla raka'a dubu.Abdullahi dan Zubair yana bayyana cewa: Ina rantsuwa da Allah lalle sun kashe Imam Husaini da ya kasance mai tsawaita sallar dare da yawan gudanar da azumi da rana. Ibnu Asakir ya nakalto cewa: Imam Husaini ya kasance mai yawan gudanar da aikin hajji, ya je aikin hajji a rayuwarsa har sau ashirin da biyar a kafa, kuma ya'yayensa suna biye da shi a baya.

  An ruwaito cewa: Idan Imam Husaini {a.s} yana alwalla launinsa ya kan canza gabobinsa suna kaduwa, sai ake tambayarsa dangane da hakan, inda ya amsa da cewa: Hakki ne a kan wanda ya tsaya a gaban Allah Madaukaki launinsa ya canja gabobinsa su kadu.

  Dabi'ar Karamci Da Sakin Hannu A Rayuwar Imam Husaini {a.s}.

  Hakika Imam Husaini {a.s} yana dauke ne da irin kyawawan dabi'un kakansa Manzon Allah {s.a.w} inda ya kasance yana da kebantaccen matsayi a wajen raunana da marassa galihu, kuma ya kasance baya da makamanci a fagen karamci da sakin hannu a zamaninsa, matsayinsa a wannan bangaren irin matsayi ne na kakansa annabin rahama Muhammadu dan Abdullahi da mahaifinsa shugaban muminai Ali dan Abi-Talib da mahaifiyarsa Fatumatuz-Zahara da dan uwansa Hasan Al-Mujtaba da 'ya'ya'yensa ma'asumai guda tara da Allah Madaukaki ya tsarkekesu daga duk wata dauda tsarkakewa.

  Imam Husaini {a.s} ya kasance yana taimakon mabukata da marassa galihu tare da nuna jin kai ga mata zaurawa da yara marayu da suka rasa mahaifansu da mazajensu a wajen yaki, kamar yadda ya kasance yana kwantar da hankalin masu neman taimako ta hanyar wadata su da kayayyakin da suke bukata, ba tare da sun ji wani kaskanci a zukatansu ba, kuma Imam Husaini {a.s} ya kasance mai tsananin sada zumunci da bada kyauta ga makusanta, inda ya kasance yana raba dukkanin abin da ya mallaka domin share hawayen jama'a da suke cikin kuncin rayuwa.

  Hakaki Imam Husaini {a.s} ya kasance yana daukan jakkunan kayayyakin abinci da na kudi a bayansa a cikin dare yana bin gidajen mata zaurawa da marayu yana raba musu wanda har ta kai ga babban makiyin Iyalan gidan Manzon Allah Mu'awiya dan Abi-Sufyan ya yi shaida da hakan; An ruwaito cewa, Mu'awiya dan Abi-Sufyan ya aike da sakon kyauta ga wasu mutane, sai ya ambaci Imam Husaini {a.s} yana cewa; Amma Husaini ya kasance yana farawa ne da raba kyautuka ga marayu da aka kashe mahaifansu a yakin Siffin, kuma idan wani abu ya yi saura sai ya soke rakuma ya raba namar kuma ya shayar da mutane madara.

  Dabi'ar Tawali'u Wato Kankantar Da Kai Da Rashin Nuna Isa A Rayuwar Imam Husaini {a.s}.

  Hakika tawali'u yana daga cikin kyawawan dabi'u masu girma, kuma ado ne da ke jan hankalin al'umma tare da saurin yin gagarumin tasiri wajen kara soyayyar mutane ga duk mai dauke da wannan siffar.

  Don haka littattafan tarihi dana hadisai suka ruwaito da dama daga cikin halayen Imam Husaini {a.s} a wannan bangaren wanda zamu ambaci kadan daga cikinsu kamar haka:-Wata rana Imam Husaini {a.s} yana shigewa sai ya tarar da wasu mabukata suna cin abinci, sai suka kira shi kan ya zo ya ci abincin tare da su, don haka sai Imam Husaini {a.s} ya sauka daga kan abin hawarsa ya zo ya zauna suka ci abincin tare, sannan Imam Husaini {a.s} ya ce musu, hakika na amsa kirarku, don haka kuma ina gayyatarku, bayan sun amince sun bi Imam Husaini {a.s} zuwa gidansa, sai ya umurci matarsa da ta fito da dukkanin abin da aka tanada a gidan na abinci, wanda ya gabatar da shi ga mabukantan.

  Har ila yau an ruwaito cewa: Wata rana Imam Husaini {a.s} yana shigewa sai ya tarar da wasu mabukata suna cin bushesshen al-kubus, sai Imam Husaini {a.s} ya yi musu sallama, bayan sun amsa sallamar sai suka gayyaci Imam Husaini {a.s} kan ya zo ya ci al-kubus din tare da su, don haka sai Imam Husaini {a.s} ya zo ya zauna tare da su, sannan ya ce musu da ba don al-kubus din da kuke ci na sadaka ba ne hakika da na ci tare da ku - saboda Iyalan gidan Manzon Allah ba su cin sadaka - sai Imam Husaini {a.s} ya gayyace su zuwa gidansa, inda ya ciyar da su tare da tufatar da su kuma ya gabatar musu da kyautan kudade.

  Yana daga cikin dabi'ar jin kai da tsananin karamcin Imam Husaini {a.s} yanta baiwa a matsayin sakamakon gaisuwa; Anas dan Malik ya ruwaito cewa ya kasance tare da Imam Husaini sai wata kuyangarsa da ta ke rike da wasu silin itacen fulawa ta zo zata shige, sai ta gaishe shi tare da gabatar masa da fulawar, sai Imam Husaini {a.s} ya ce; Je ki ke 'yantacciya ce domin Allah, sai Anas dan Malik ya zabura ya ce; Baiwa ta gaida ka da wasu silin fulawa sai ka 'yanta ta? Sai Imam Husaini {a.s} ya amsa da cewa: Kamar haka ne Allah ya ladabtar da mu, inda yake bayyana cewa:"Kuma idan aka gaishe ku da wata gaisuwa, to sai ku amsa da wadda ta fi ta kyau ko kuma ku mayar da irinta".

  Sannan Imam Husaini {a.s} ya kara da cewa; Hakika abin da ya fi zama mai kyau daga gaisuwarta shi ne 'yantar da ita daga kangin bauta.

  Dabi'ar Imam Husaini {a.s} A Bangaren Tsananin Hakuri Da Hadiye Fushi.

  Tsananin hakuri da hadiye fushi suna nufin rashin tasirantuwa da duk wani abin da ke tunzura mutum ga bacin rai ko kufula.

  Hakika wadannan halaye biyu suna daga cikin kyawawan dabi'u madaukaka da kima, kuma dabi'u ne da suke kai mutum ga babban matsayi da kamala a rayuwa, don haka Imam Husaini {a.s} da ya kasance ya tasirantu da kyawawan dabi'un kakansa Manzon Allah {s.a.w} ya shahara da wadannan dabi'u a rayuwarsa kuma ya kasance fitila ga al'umma a wannan bangaren. An ruwaito cewa: Wata rana daya daga cikin bayin Imam Husaini {a.s} ya yi masa laifi da ya cancanci ladabtarwa, don haka Imam Husaini {a.s} ya bada umurnin ladabtar da shi, sai bawan nan ya ce; Ya shugaba na, Allah Madaukaki yana cewa: "Da masu hadiye fushi" sai Imam Husaini {a.s} ya ce; a kyale shi, hakika na yi hakuri.

  Sannan bawan nan ya sake furta fadin Allah da ke cewa: "Da masu yin ahuwa ga mutane" sai Imam Husaini {a.s} ya ce; hakika na yafe maka. Sannan bawan nan ya sake furta fadin Allah da ke cewa: "Kuma Allah yana son masu kyautatawa" sai Imam Husaini {a.s} ya ce; je ka na yanta ka domin Allah, kuma kana da ninkin abin da na kasance ina baka na taimako.

  Ya zo cikin littafin Ihkakul-Hakk cewa: Imam Husaini {a.s} yana bayyana cewa da mutum zai zage ni a kunne na na dama sannan ya kewaya ya nemi uzuri na a kunne na hagun, da na yafe masa, domin shugaban muminai Imam Ali dan Abi-Talib {a.s} ya bayyana mini cewa ya ji kaka na Manzon Allah {s.a.w} yana cewa duk wanda baya karbar uzuri daga mutumin kirki ko wanda ma ba na kirki ba ne, ba zai riske ni a bakin tafki na ba a ranar kiyama.

  #ObeyCourtOder
  #🆓Zakzaky
  AllahProtecZakzak

  To find out detailed information on the event of Ahlul-Bayt (As), visit:

  🌐Webside
  Isiyasy.blogspot.com
  Isiyasy.WordPress.com

  💠 Telegram 
  http://t.me/F5StarMedia
  https://t.me/F5StarsMediaGroup

  https://mobile.twitter.com/Isiyasy
  http://mobile.fb.me/F5StarsMedia/ 

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#