ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Wednesday, 3 April 2019

  Kissar Isra'i da Mi'iraji Manzon Allah (S)


  yadda isra'I da  mi'araji da Manzon Allah  ya kasance kamar yadda yazo a farkon suratul isara;I Inda

  Allah Madaukakin sarki yake cewa tsarki ya tabbata ga wannan da yayi isra'I da
  bawansa cikin Dare daga masallacin harami wato makka zuwa masallacin kudus wanda muka albarkaci kewayensa domin mu nuna masa daga cikin ayoyin mu hakika Allah ya kasance maiji ne kuma mai gani

  To sai dai akwai sabani tsakanin malamai game da batun wuri da lokacin da akayi Isra'I da mi'iraji kwararran malamin nan mai bincike da aka fi sani da muhakikik subuhani ya bayyana cewa batun mi'araji

  Shine salloli biyar din nan da aka wajbtama kowanne musulmi yayi su a kowacce rana, domin tun bayan rasuwar kawun Manzon Allah.

  Wato Abu talib kenan ashekara ta goma da aiko manzo tsira,kuma babban dalili akan haka shine a daren mi'araji din ne Allah madaukakin Sarki ya saukar da wahayi ga Manzon Allah ya umarci musulmi su rika yin sallah sau biyar a rana.

  Don har lokacin da Abu talib ya rasu yin sallah biyar ko wace rana bata zama
  wajibi ba, domin a lokacin babban nauyin
  da ya doru a kan manzon Allah shine ya
  kira mutane suyi furuci da kalmar
  shahada amma batun salla da babu wani
  labari akai, amma batun yadda isar'I ya
  kasance da jiki ne ko kuma da ruhi akwai
  bahasi mai yawa tsakanin malamai amma abinda yazo a zahirin kur'ani shine da jiki .

  amma kissar da tafi shahara game da batun yadda isra'I da mi'iraji ta kasance shine lokacin da manzon Allah yake garin makka acikin dare sai yana farkawa sai ya ganshi a masallacin kudus cikin ikon ubangiji, kamar yadda yazo acikin ruwayar akan yanyarsa ta tafiyawa zuwa Masallacin qudus shi da Mala'ika jibrilu sun sauka a garin madina domin yin sallah haka kuma ya kasance tare dashi a masallacin qudus inda a nan ma ya hadu da manyan Annabawan Allah da suka gabata kamar Annabi Ibarahim da musa da Isa kuma manzon Allah ne ya jagoranci sallar.

  To daga nan kuma sai ya tafi zuwa sama yaje dukkanin sammai bakwai da ake dasu yaga abinda ke cikin sun na ban mamaki da al'ajabi da hankalin dan adam ba zai taba kai wa zuwa gareshi ba inda yaga wasu annabawan a cikin wasu sammai din, yayi ido 2 da wadanda ke cikin aljannah .

  daga nan ne ya kai sama ta bakwai inda
  ya keta hijabai na haske har ya kai
  Sidiratul muntaha da kuma jannatul
  ma'awa inda yayi nusto a cikin haske da
  hijabai na badini har dai ya kusanci zatin
  ubangijin Madaukaki tsarki ya tabbata
  gareshi, ya kai matsayi na makama
  kaba kausaini au adna,

  Acikin wata ruwayar kuma yazo cewa wata rana Dare ya fara gushewa haske na Asubahi ya fara bayyana sai Ummu hani taji alamar sautin munajati da Manzon Allah (S) ya keyi inda kamshi na ma'anawiya ya lullube gidan a lokacin tana cikin sallar Asubahi amma sai ta fahimci cewa lallai akwai wani muhimmin al'amari da yake faruwa kuma lallai manzon Allah yana son ganinta nan da nan sai Ummi hani ta mike ta kama hanya taje kusa da manzon Allah sai ya bayyana mata cewa kin sani cewa daren jiya anan nayi sallar Isha'I to bayan nan Mala'ika Jibril yazo da wata buraka ya kaini baitul mukkadas daga nan kuma mukayi tafiya zuwa sama inda naga mala'iku suna cikin farin ciki da annashawa akan ziyarar tawa kuma na tafi zuwa wurare da yawa a sama, kuma nayi sallah a massallacin qudus kuma na ga Guraben Annabawan Allah kuma gashi dai kamar yadda kika gani a nan.

  Nayi sallar Asubahi, sai Ummi hani yar uwa kuma Matar kawun Manzon Allah ta fada cikin damuwa ta fadi cewa labarin da ka bani yafi rana bayyana a wajena Amman na rantse maka da ubangijin duniyar nan wanda rainake hannunsa ba zan taba gayawa wani mahaluki wannan labari da ka bani ba, zanyi gum da baki na, sai Manzon Allah ya cika da farinciki, cikin murmushi yace ni yanzu inaso inje inga kuraishawa domin in basu wannan labari domin su fahimci girma da kudurar
  Ubangiji sai ummi hani ta rike manzon
  Allah bata so ya tafi tace yanzu za kaje
  wajen mutanen da ba suyi imani da sakon da kazo musu dashi ba, sun karyata ka akan gaskiyar da kazo musu da ita ?

  Ina tsoron kada wadan nan mutane su cutar da kai, to Sai dai bai ce mata uffan ba ya fice daga gidan ummu hani, lokacin da manzon Allah ya tunkaro masallaci sai
  ya ga yana cike da mutane sun shagaltu
  da labari tsakanin su lokacin da Abu Jahal ya ga Manzon Allah sai ya daga kai kamar yadda ya sa ba cikin Izgili yace:

  Ya mohammad shin kana dauke da wani sabon labari ne ? sai Manzon Allah ya bashi Amsa cewa jiya nayi Mi'iraji ,zuwa sama, cikin al'ajabi sai Abu Jahil yace ina aka kai ka ?

  Sai manzo Yace zuwa masallacin qudus sai yace kana nufin daren jiya ka tafi masallacin qudus amma kuma har ka dawo gashi yanzu kana cikin mu ?

  Ai sai Abu jahal ya bushe da dariya ya kwada kira yace kuzo kuji abinda Moh'du yake cewa , nan take sai mutane suka zaburo suka kewaye su sai Manzo Allah yace a jiye da dare na tafi baitul mukaddas kuma naga wasu daga cikin Annabawan Allah kamar Annabi Isa , Musa Ibarahim As
  kuma nayi magana dasu kuma munyi sallah tare, kuma nine na jagorancin sallar
  kuma naga Abal Bashar Annabi Adamu
  As.

  Lokacin da ya kalli daman sa sai yayi farin ciki lokacin daya kalli hagun sa kuma sai yayi bakin ciki sai nace ya jibrilu menene haka ?

  Sai yace duk lokacin da naga an kai wani dan Adam Aljanna sai farin ciki ya kama ni amma duk lokacin da naga an kai wani dan Adam gidan wuta sai bakicin ciki da bacin rai ya kama ni wannan shine dalilan da yasa kake ganin isan na kalli wani bangare sai inyi murmushi idan na kalli wata kusurwar kuwa sai nayi ji bacin rai.

  Sai wani mutum mai suna Mad'am bin
  Adi ya tambayeshi cewa shin kana nufin tafiyar wata biyu ce kayi ta a cikin dare
  daya ?

  Sai Manzon Allah yace masa tabbas
  domin a cikin wannan daren a lokacin da nake tafiya naga ayarin yan kasuwa
  wanda sautin karan burakar dana ke kai ta
  tsorata su har ma suka tarwaste wani daga cikin su ma ya bace basu ganshi ba, har ma na kama wanda ya bace din na kaishi inda rakumin shi yake a wannan lokacin suna kan hanyar sham ne akan hanyarsu ta dawowa gida don ma yanzu suna gab da makka haka zalika na sake haduwa da wata tawagar amma dukkan mutanen suna barci kuma suna da wani kwano shudi har ma na dauki gorar su na sha ruwan dake ciki kana na a jiye musu suma yanzu haka suna gab da isowa makka kuma ma jagoransu dake gaba wani rakumi ne mai ruwan kasa kasa
  wanda akwai wasu dabbobi fari da baki
  suna biye dashi


  1 comment:

  1. duk abinda kaji annabi yafada gaske ne ko ya aikata ko aka aikata agabansa bai hanaba, wannan labari yana cike da abin mamakin da dunia bata taba ji ko gani ba. Allah ya qarawa annabinmu daraja.

   ReplyDelete

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#