Hadisi na 52
Daga zaid (RA) shi kuma daga Abi-Abdullahi (as) yace bazaku ta6a zamowa muminai ba har sai idan kun zamo amintattu a wurin mutane kuma sai kuna ganin yalwar Ni'ima a mastayin masifa domin yin hakuri a kan bala'I shi yafi akan walwala cikin jin dadi
DARASI
Abin da wannan hadisi ke karantarwa shi ne kafin mutum ya zama mumini to dole ne sai mutane sun aminta da gaskiya da rikon amanarsa sai mutane sun gamsu da dabi'unsa na rashin cin amana rashin ha'inci da rashin yaudarasa.
Sannan cikekken mumini shine mai fifita jarabawa a kan zama cikin walwala da nishadi domin ita jarabawa ta fi damfara zuciyar bawa ga Allah amma jin dadi da walwala kan janyo wa mutun gafala da rafkana da sakaci
______S.Y_______
No comments:
Post a comment
Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun