Inna lillahi wa inna ilaihi Raji'un!!!
ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜
Hashim Badikko
A safiyar jiya ne 12 Rajab, 1442 h, wanda ya yi daidai da 24/02/2021 muka wayi gari da labari mai tada hankali, mai girgiza zukata na rasuwar ÆŠalibarmu; Malama Husaina Sani Nasarawa.
Haƙiƙa wannan rashin na mu ne gaba ɗaya, ba na Iyaye ko Miji bene kawai.
Husaina Sani ta kasance tare da mu a Makarantarmu ta A'alamul Huda tun daga ranar da aka buÉ—e ta har izuwa ranar Rasuwarta.
Allah Sarki Mutuwa! Ba ta barin wani don wani, ta É—auke jaririn dake cikin Mahaifiyarsa kafin ya fito duniya, ta kuma É—auke Uwa da bar Jaririnta bayan fitowarsa duniya; kamar yadda ya faru da Malama Husaina Sani.
Duniya ba gidan dawwama ba ce, gida ne ga wanda ba shi da gida.
Allah (swt) bai yi alƙawarin dawwamar da ita ba, duk abin da ke cikin zai ƙare, babu mai wanzuwa.
Malama Husaina! Ba ke muke wa kuka ba, muna yi wa kan mu ne. Ke, ta ki tayi kyau kamar yadda naji Annabina Muhammad (sawa) ya yana faÉ—i.
Malama Husaina! Kin yi Shahada kin huta. Kin ci ribar rayuwa. Kowa ya buÉ—i baki sai ka ji alheranki yake faÉ—i.
Kin koma ga Allah da Wilayar Ahlul Bait (as), kin yi babban guzurin da baya ƙarewa. Ko ba ta sanadiyyar haihuwa ki ka rasu ba; za mu iya kiranki Shahidiya saboda kin rasu akan Soyayyar Ahlul Bait (as), balle kuma kin haɗa biyu, ga Soyayyar Ahlul Bait (as), ga kuma rasuwa ta hanyar Shahada!!!.
Muna shirin yin Walimar gama karatu da suka yi a sashen Diploma na Jami'atul Mustafa (sawa), ashe ba za ta shaidi wannan ranar ba da gangan jikinta. Ashe karatunta ya wuce na mu!!!. Husaina tunda kin gama karatu da mu, ranar walima haka za mu aje miki kujerar ki a cikin sahun Ƴan Ajinku, tare da shaidar kammalawa!!!
Ya Allah ga BaƙuwarKa nan, wacce ta shaida babu abin bauta da gaskiya sai Kai, ta kuma shaida AnnabinKa Muhammad (sawa) shine Manzon da ka aiko, ta kuma shaida cewa A'immah na Ahlul Bait (as) 12 sune Jagorori bayan ManzonKa (sawa).
Ya Allah! Ba mu san komai game da ita ba sai Alheri.
Ya Rasulallah! Ga Baiwar Gidanku nan, ayi mata Masauki, don Kaine mafi Alherin masu Masu Masaukai.
Ya Limaman shiriya! Ga Masoyiyarku nan, wacce tayi riƙo da ku a duk tsawon rayuwarta, ayi riƙo da hannayenta. Ba ta da kowa sai ku.
Malama Husaina! Muna son ki, amma Allah Ya fi mu son ki. Sai mun sake haÉ—uwar da babu rabuwa a cikinta.
Ba kiyi gaggawa ba, mu kuma ba mu yi nawa ba.
Muna miki ban kwana! Sai mun zo.
Wadá'an👋.
Hashim Badikko
No comments:
Post a comment
Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun