ads header
 • Breaking News

  5Five Stars Media News And Education You Are Welcome

  .

  Sunday, 7 February 2021

  Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Malaman Kano

   Nasarar ilmi da hankali, a kan jahilci da takobi.

   Hashim Badikko

  Tarihin ɗan Adam ba zai taɓa cika ba, ba tare da an ambaci irin baƙin zaluncin da aka yi wa Ahlul Bait (as) ba. 

  A tsawon tarihi, babu lokacin da aka sarara masu, tun daga kan Shugaba Manzon Rahma, Annabi Muhammad (sawa) har zuwa 'Ya'ya da jikokinSa.

  Banu Umayya sun yi duk abin da za su iya yi a tsawon watanni dubu don ganin sun shafe hasken Gidan Annabta, amma ta Allah, ba ta su ba.

  Bayan shuɗewar su kuma, sai Banul Abbas suka ɗora daga inda suka tsaya. Ahlul Bait (as) sun fuskanci tsananin gaske, ta hanyar kora daga gari, ɗauri, da ma kisan gilla, amma Allah Ya wanzar da ambatonsu.

  Tarihi ba zai manta da irin ƙuncin da aka saka su da Mabiyansu a ciki ba. Wannan ya tilasta masu barin Mahaifarsu (Madina) zuwa wasu garuruwa daban-daban. 

  An raba su da al'umma ƙarfi da yaji, babu kowa tare da su sai 'yan kaɗan, su ma ɗin sun fuskanci kora da kisa daga mahukuntan wancan lokacin.

  An koya wa al'umma tsine masu a lokutan kiran Sallah, da kuma kan Minbarori a lokutan huɗuba.

  Duniya ta yi duhu da irin wannan baƙin zaluncin da aka yi masu. 

  Wannan zaluncin bai tsaya a wancan lokacin ba kawai, a'a, ya ci gaba har zuwa yau ɗin nan.  

  Duk da wasicin da  Manzon Allah (sawa) Ya bar mana na riƙo da Al-Ƙur'ani da Ahlul Bait (as), amma al'umma ta bijire, sakamakon mummunar fassara da ƙarairayi da wasu Malaman Fada na wancan lokaci suka yi wa al'umma a kan haka.

  Har an wayi gari Musulmi yana kunya, ko kyama, ko kuma tsoron a danganta shi da su, saboda yadda aka munana su a idon duniya. 

  A irin wannan hali ne kuma tarihi ya sake maimaita kansa, Umayyanci ya sake dawowa, inda aka samu wasu Malamai a Kano, waɗanda iilminsu ya kasa kwatarsu, suka yi amfanin da ƙarfin fada-aji a wurin hukumomi, suka zartar da hukuncin zalunci a kan Babban Malami, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ta hanyar rufe makarantu da masallatansa, da kuma yi masa ɗaurin talala.

  Lallai ilmi da hankali sun yi nasara a kan jahilci da takobi, Sheikh Abduljabbar ya sa ilmi, ku kuma kun sa jahilci, ya sa hankali, kun yi amfani da hukuma an sa masa takobi.

  Watakila ina da nazari da ra'ayi a kan Manhaj da uslub ɗin Maulana Sheikh Abduljabbar, Watakila ina da nazari da ra'ayi a kan wasu Maudu'an da yake tattaunawa a matsayina na Hashim Badikko mai ƙarancin sani, kuma ɗalibi a Makarantar Ahlul Bait (as), amma wannan ko kusa ba ya nufin yadda da zaluntarsa da ake yi, ko rashin kasancewa tare da shi. Ina tare da shi ɗari bisa ɗari. Saboda na san abin da ya sa ake masa wannan baƙin zaluncin. Kuma har abada ba zan karkata zuwa ga azzalumai ba. 

   Baƙin Albishiri
  Za ku iya amfani da jahilcin mabiyanku, ku yi galaba na ɗan wani lokaci, amma ƙarshen al'amari nasara tana tare da masu Taƙwa ne.

  Sheikh Abduljabbar ya yi muku ƙalubalen cewa ku zo a zauna, a tattauna, a fid da tsakuwa daga aya, amma kun yi mursisi, kun ce atafau, sai dai a hana shi magana, ko kuma a kashe muku shi.

  Baƙin albishirin da nake muku shi ne; kun sa an  kashe maciji ne, amma ba a sare muku kan ba. Kun makara har ɗan Zaki ya girma.

  Ko da burinku zai cika a kan Sheikh Abduljabbar, to ku sani, ya riga ya yi galaba a kan ku, kuma da sannu za ku yi nadama a lokacin da nadamar ba ta da amfani. 

  Kun yi jana'izar ilmi da bincike (bahsi), kun kawo ƙarshen taɗawwur na ilmi, kun kawo ƙarshen ilmin Musɗalawul hadith, ko ulumu hadith. In da da kunya ba za ku ƙara karantar da duk Maudu'an da ke cikin wancan ilmin da na kawo a sama ba, balle har ku ce akwai Hadisi Da'ifi, ko Hasan, ko Maudu'i ba. Kun san abin da nake nufi. Allah dai ya kyauta.

  Me ya sa ba ku da yaren da kuka iya sai na zubar da jini? Har babban cikinku, wanda baƙon haure ne, yana cewa in da za su samu dama da sun kashe shi!

  Yar yanzun jinin da yake zuba a ƙasashen duniya saboda irin karantarwarku bai ishe ku ba? Kun hana duniya zama lafiya, kun kasa zama da wanda ya saɓa da ku a ra'ayi, ko dai mutum ya bi ku, ko kuma ku sa a kashe shi kamar yadda ɗaya daga cikinku ya faɗa Sakkwato.

   Allah ba azzalumi bane, yana a madakata.

  Kun yi wa al'ummarku ƙarya, kun murguɗa zance kamar yadda kuka saba a tsawon tarihi. Sheikh Abduljabbar kare martabar Manzon Allah (sawa) yake yi, da ƙoƙarin tunkuɗe masa dattin da aka jinjina gare shi, amma kuka murguɗa zancen alhali kuna sane, ku ka cewa al'ummarku, waɗanda kuka hana su tunani da kan su, wai shi ne ma yake zagin Ma'aiki (sawa)! Ku sani, Allah yana a madaka. Kun yi na ku, ku saurari na Allah.

  Yadda kuka ci amanar al'umma, kuka yaudare su, kuka ɗaura su a kan ƙarya, to tambaya a nan, shin za ku iya yaudarar Allah ne?. Allah dai ba mutum bane da za ku iya yaudarSa, bai yadda da zalunci ba, kuma ba ya shiryar da mutane azzalumai.

   Gwamnan Kano
  Ina da yaƙini cewa ba yadda za a yi ka yi wa Sheikh Abduljabbar adalci, na ma ga ƙoƙarinka da har aka ɗauki tsawon wannan  lokacin kafin ka ɗau mataki a kan sa.

  Sheikh Abduljabbar ya ƙi yadda ya ci amanar jama'ar Jihar Kano ta hanyar ba ka kariya, bayan an gan ka dumu-dumu kana kwasar abin da ake zargi dalolin al'ummar Kano ne kana zubawa a Malum-malum. Ka nemi shi da ya fito ya nuna cewa ƙarya ake maka, har da tayin miliyoyin kuɗi, amma ya ƙi ƙarba, tunda kun kasa tabbatar masa da cewa sharri ake maka. Tun a lokacin na san cewa sai ka bi shi da mummunar makida bayan ka murguɗe zaɓe. Na rantse da Allah ba abin da za ka yi masa in yi mamaki, don ka yi abin da ya fi wannan.

  In da gaske kai Gwamnan kowa da kowa ne, da sai ka sa a yi bincike, a kuma tattara dukkan Malaman da suke da ƙorafi a kan Sheikh Abduljabbar, (kamar yadda shi da kan sa ya nemi a yi haka, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba), su zauna a yi muƙabala. Amma sai ba a yi haka ba, sai kawai aka dakatar da shi, da kuma rufe dukkkanin makarantunsa, wai kafin a gama bincike, kamar yadda Kwamishinan Yada Labarai, Muhammad Garba ya faɗa.

  To tambaya, wane bincike kuma za a yi, alhali a jawabin Gwamna ya riga ya nuna cewa shi ne mai laifi, yana harzuƙa al'umma a kan su ɗau mataki a kan sa, kuma kada a ji tausayinsa? 

   Shawara 
  Duk Malaman da suke da hannu a kan wannan zaluncin da aka yi wa Sheikh Abduljabbar su sani, bayan wannan rayuwar akwai lahira, kuma duniyar da kuke nema da jinin wasu, ba za ku same ta ba. Kuma ko kun samu, kwana nawa za ta yi muku? Ku ma ku saurari bayyanar Zakokin da ba za ku iya tarar su ba Wallahi behold

   Shawara ga Hukuma 
  Gwamnatin Kano ta sani, waɗannan Malaman ba 'yan goyo bane, yanzun suna yi da ku ne saboda ku kuke a kan mulki, da zarar 'yan adawa sun hau, za su koma wajensu, su kuma zage ku. Kamar ƙudaje suke, duk inda kwaɗayi yake; nan suke. Ko za a wulaƙanta su, in dai za a ba su na ƙashin miya, sai sun je. Kun dai san abin da ya faru tasakaninsu da tsohon Gwamnan Kano, Alhaji Rabi'u Musa Kwankwaso.

  Sannan a ƙarshe ina son Gwamna ya san cewa Mulki yana tabbata da adalci, amma ba ya tabbata da zalunci. 

   Muna kira a yi adalci.

  Amincin Allah ya tabbata ga waɗanda suka bi shiriya.


   Hashim Badikko
  yusufgarba1986@gmail.com

  No comments:

  Post a comment

  Comment For This Post/Yi Tsokaci Akan Wannan Rubutun

  Translate - Fassara

  Buy Data Online

  Now You Can Buy Your Cheap Internet /Mobile Data plan Very Discount Prices @At 5Five Stars Media.

  Yanzu Zaku Iya Sayan Data Mai Sauki Na Yanar Gizo-gizo Na Wayar Salula A 5Five Stars Media

  9mobile 100MB N100

  9mobile 200MB N200


  9mobile 500MB N500


  9mobile 1GB N750
  1GB N550


  2GB N1100


  Yadda zaka duba data balance dinka
  MTN: *461*4#
  9Mobile: *228# Or *229*9#